Warwarewa labaran bogi da CDD ta aiwatar daga 31 a watan mayu zuwa 7 ga watan yuni shekara ta 2020

Shin Shugaba Buhari Ya Kori Hafsoshin Rundunonin Tsaron Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 29 ga watan Mayun shekara ta 2020, jaridar Daily Mail Online ta wallafa wani labari dake cewa Shuagab Muhammadu Buhari ya kori hafsoshin rundoninin tsaron kasar nan sakamakon almundahanar da ta shafi kudade.

Labarin ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya salami manyan jami’an tsaron ne bayan aka gabatar korafi akansu day a shafi aikata cin hanci da rashawa.

Labarin harwayau ya kara da cewa tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari ya rufe almundahanar da hafsoshin tsaron suka tafka.

Wani shafin yanar gizo mai suna Will a wani labari da ya wallafa shima ya yace Shugaba Buhari ya amince da korar manya shugabannin rundunonin tsaron ne bayan cin hanci da rashawar da suka tafka ta fito fili makonni bayan rasuwar Malam Abba Kyari.

Kamar yadda shafin yanar gizo na Will din ya zayyana, marigayi Abba Kyari a lokacin rayuwar sa akodayaushe yana boye cin hanci da rashawar da hafsoshin tsaron ke tafakawa.

Gaskiyar Magana:

Binciken da masu tantance sahihancin labari na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD batun korar hafsoshin rundunonin tsaron ya samo asali ne daga jita-jitar da ake yadawa a sassa daban-daban na kasar nan.

CDD har wayau ta gano cewa Shugaba Buhari baiyi kowane irin furuci ba game da hafsoshin rundunonin tsaron wadanda suka kama aiki tun shekata ta 2015.

Wani bincike da CDD din ta aiwatar ya gano cewa shugaban rundunar sojan kasan Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai yaje Maiduguri a Jahar Borno a ranar Asabar, 30 ga watan Mayun shekara ta 2020 dan ganin yadda kirkira dama gyara ababan sufuri da akanyi anfani dasu a lokacin yaki da wassu injiniyoyi ke aiwatar wa. Domin Karin bayani latsa nan https://www.cddwestafrica.org/shin-shugaba-buhari-ya-kori-hafsoshin-rundunonin-tsaron-najeriya/

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

Labarin da aka Wallafa Cewa Shugaba Buhari Yayiwa Tsohuwa Yar Shekaru 70 Fyade A Shekarun Baya Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Labara, 3 ga watan Yunin shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba sun gano wani labari da wassu shafukan yanar gizo guda biyu suka wallafa cewa wata tsohuwa yar shekara 70 tana zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari dayi mata fyade a shekarun baya.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Shugaba Buhari ya aikata lamarin ne a shaekara 1972.

Ga yadda aka gina jigon labarin: “acikin hoto mai motsi (bidiyo) wata tsohuwa tayi zargin cewa Shsugaba Buhari yayi mata fyade a shekarar 1972, wannan bidiyo yana shan kallo, gama hotuna dan Karin bayani”

Jim kadan da wallafa wannan labari, mutane sama da dubu daya ne suka karanta shi yayi wassu mutane 800 sukayi mu’amila dashi kawo lokacin hada wannan tantancewa.

Gaskiyar Magana:

Bayan da masu tantance sahihancin labari na CDD suka gano jan hankalin da labari yake yi sun gudanar da bincike game da inda labarin ya samo asali sai suka gano cewa wassu zauran yanar gizo da suka yi suna wajen kirkira da yada labaran karya ne suka wallafa shi. Zaurukan sune: Cyoungblogs da Legitfund. 

Ko a watan Afirilun day a gabata saida daya daga cikin zaurukan ya wallafa wani labarin bogi inda yace: “Na rabawa dukkan yan Najeriya  naira dubu 5000 ta hanyar anfani da kariyar su ta BVN-inji Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo. Bayan wallafa wannan labari CDD ta aiwatar da bincike inda ta gano cewa labari ne na bogi kuma ta wayar da kan jama’a game dashi.

Binciken CDD ya gano cewa Cyoungblogs suna wallafa labari ne a wani kanfani mai suna Golden Media Nigeria wanda ke mabiya dubu dari takwas (800,000) a dandalin Facebook kuma sunyi suna wajen wallafa labaran karya dama jirkitattun labarai. Domin Karin bayani latsa nan https://www.cddwestafrica.org/labarin-da-aka-wallafa-cewa-shugaba-buhari-yayiwa-tsohuwa-yar-shekaru-70-fyade-a-shekarun-baya-karya-ne/

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar

Shin Majalisar Dinkin Duniya Na Shirin Kirikirar Sabuwar Kasa Daga Kasashen Najeriya Da Kamaru?

Tantancewar CDD: Karya Ne!

Tushen Magana:

Majiyoyi da yawa sun wallafa rahotonnin dake cewa Majalisar dinkin Duniya zata kirikiri sabuwar kasa daga yankunan kasashen Najeriya da Kamaru a ranar 10 ga watan Yulin shekara ta 2020.

Sunan sabuwar kasar inji rahotannin zai kasance UN Organisation State of Cameroon.

Jaridar Guardian da ake wallafawa a Najeriya tace kirkiran wannan kasa zai kai Najeriya ga rasa kananan hukumomi 24 da Tsohon Shugaba Obasanjo ya sallamawa Shaugaba Paul Biya na Kamarun a baya.

Gaskiyar Magana:

Wannan batu babu gaskiya acikin tunda Majalisar Dinkin Duniya bata da yancin kirkiran wata kasa daga wassu kasashe dake wanzuwa.

Ita wannan kasa da aketa tababa akanta ta UN Organisation State of Cameroon bata cika sharudan da ake yiwa lakabi da the Montevideo Convention wanda suka bukaci cewa babu wata da take da yancin yiwa wata katsalidin acikin harkokinta na ciki ko wajenta.

Har wayau ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya bayyana rashin masaniyar sa game kirkiran sabuar kasar.

Wani rahoton shirin AIT Live ya bayyana tuntubar wata majiya daga Majalisar dinkin Duniya wanda tayi watsi da labarin kuma ta bayyana shi a matsayin na bogi ta kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya bata kirkiran kasashe. Domin Karin bayani latsa nan https://www.cddwestafrica.org/shin-majalisar-dinkin-duniya-na-shirin-kirikirar-sabuwar-kasa-daga-kasashen-najeriya-da-kamaru/