Shin Sipetan Yan Sandan Najeriya Ya Mika Ragamar Hukumar Yan Sanda Ga Mai Rikon Kwarya?

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 2 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani zauren yanar gizo mai suna OperaNews ya wallafa inda yace Sipetan Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu mika ragamar mulki ga sabon sipetan yan sanda da zai maye gurbin sa.

Labarin yace Sipeta Adamu ya cika shekaru 35 da kama aikin gwamnati dan ya mika ragamar hukumar yan sanda ga mataimakin sa mai kula da harkokin yau da kullum mai suna Sanusi Lemo.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa kawo ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekara ta 2021 Mohammed Adamu shine Sipetan Yan Sandan Najeriya. Labarin da ke cewa ya mika ragamar shugabanci ga mataimakin sa ba gaskiya bane.

Da yake maida martani ga labarin, mai magana da yawun yan sandan Najeriya Frank Mba a wata hiar da yayi da jaridar Nation ranar 2 ga wata Fabrairu yace rahoton da ke yawo cewa sipetan yan sanda Mohammed Adamu ya mika shugabanci ga DIG Lemo ba gaskiya bane, dan haka jama’a suyi watsi da labarin. Kawo lokacin hada wannan rahoto ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, Shugaba Muhammadu Buhari bai ayyana wanda zai jagoranci hukumar yan sandan dan maye gurbin Mohammed Adamu ba.

Kammalawa:

Jita-jitar da ake yadawa cewa Sipetan Yan Sandan Najeriya Mohammaed Adamu ya mika jagorancin ma’iakatar yan sanda ga wanda zai rike ma’aikatar na wucin gadi ba gaskiya bane.

Kawon lokacin hada wannan rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, Mohammed Adamu ne ke ci gaba da zama Sipetan Yan Sandan Najeriya.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa