Shin Rundunar Yan Sanda a Jahar Kano ta Hana Gudanar Da Tashe?

Gaskiyar Magana: Eh, Hakane!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 21 ga wtaan Afirilun shekara ta 2021 rahotanni game da hana tashe a  jahar Kano sun karade shafukan yanar gizo. Rahotannin sunce rundunar yan sanda a jahar Kano ta sanar da hana gabatar da wasan tashe acikin watan Ramadan a jahar Kano.

Rahotannin wadan da majiyoyi da suka hada da Rahma TV suka rawaito sun bayyana cewa an hana tashen ne saboda magance laifuffuka da ake aikatawa lokacin gabatar da tashen.

Gaskiyar Al’amari:

Labarin da ake yadawa cewa rundunar yan sandan jahar Kano ta hana gudanar da tashe acikin watan azumi gaskiya ne. Binciken CDD ya gano cewa hanin ya fito daga rundunar yan sandan Kanon.  Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa CDD matsalolin da suka sa yan sandan suka aiyana hanin. A cewar sa batagari na amfani da tashen wajen aikata miyagun lafuka acikin al’umma.

DSP Kiyawa ya ce: “hana tashen bai shafi tashen da kananan yara za su gudanar ba”

“Tashen da aka hana shine wanda matasa ke aiwatarwa wanda ke janyo sace-sacen wayoyi da sauran kadarorin jama’a dama fadan daba. An dauki matakin hana tashen ne dan magance wadannan laifuffuka da ake aikatawa yayin gudanar da tashen”

Kammalawa:

Labarin da ake yadwa cewa rundunar yan sanda a jahar Kano ta hana gudanar da tashe acikin watan azumi gaskiya ne. Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace hanin bai shafi tashen da kananan yara ke aiwatar ba. An hana tashen da matasa ke gudanarwa ne dan magance miyagun laifuka da tashin hankali da ke faruwa lokacin da matasan ke gudanar da tashen.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa