Shin Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Hukumar Zabe a Jahar Edo?

Gaskiyar Magana: Labarin Yana Cike Da Rudani!

Da misalign karfe 8:30 na safiyar yau Asabat, 19 ga watan Satunban shekara ta 2020 jaridar Vanguard ta wallafa wani labari  mai taken: “Jami’an tsaro sun mamaye hukumar zabe a jahar Edo”.

Gaskiyar Magana:

An jibge ayarin jami’an tsaro a hedikwatar hukumar zabe ta kasa INEC dake birnin Benin a jahar Edo tun ranar 17 ga watan Satunban shekara ta 2020. Hadin gwiwar jami’an tsaro daga hukumomin tsaro daban-daban ne aka samar a hukumar zaben dan samar da tsaro kafin da lokaci dama bayan zaben gwamnan dake gudana a jahar Edon. Masu lura da yadda zaben ke gudana sun tabbatar da kamai yana tafiya daidai, dan haka labarin cewa jami’an tsaro sun mamaye hukumar zaben yana cike da rudani. Jami’an tsaron da aka jibge a hukumar zaben an samar dasu ne dan bada tsaro ga hukumar.

Kammalawa:

Labarin da jaridar Vanguard ta buga cewa jami’an tsaro sun mamaye hukumar zabe a jahar Edo yana cike da rudani.

CDD tana jan hankalin kafafen yada labarai da su guji bada labari ta hanyar jefa rudani a zukutan mutane dama gina labari da jigon da zai iya haifar da.

AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa