Shin Hydroxychloroquine Yana Maganin Cutar Corona?

Tantancewar CDD: Babu Kwakwkwarar Hujja Da Ta Nuna Hakan!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 27 ga watan Yulin shelara ta 2020, wani faifan bidiyo ya yadu matuka gaya a kafafen sada zumunta a Najeriya, acikin bidiyon anga wata likita yar asalin Najeriya dake zaune a kasar Amurka.

Bidiyon wanda tun farko wata kafar yada labarai mai suna “Breitbart News” ta wallafa ya nuna wassu mutane sanye da kayan masu bincike a dakin gwaje-gwajen dan gano matsalolin lafiya wanda kuma kira kansu “America’s Frontline Doctors” a wani taron manema labarai a gaban babbar kotun Amurka dake birnin Washington DC.

Acikin bidiyon, mai wa’azi kuma jami’ar lafiya Stella, tayi wani jawabi mai karfafa gwiwa inda tace hydroxychloroquine, wanda maganin zazzabin cizon sauro ne zai magance cutar Corona da ta addabi duniya.

Stella ta kara da cewa tayi anfani da hydroxychloroquine da zinc da Zithromax (Azithromycin) akan mutane masu dauke da cutar Corona da yawan su yakai 350 kuma duk sun warke a asibitin ta.

Jami’ar lafiya Stella, ta kara da cewa hydroxychloroquine yana maganin cutar da ta shafi matsalar matsanancin nunfashi da a turance ake kira Severe Acute Respiratory Syndrome Coronavirus 2 (SARS-CoV-2).

Stella ta kuma yi maganar cewa mutane basa bukatar takunkumin rufe hanci da baki dan neman kariya daga cutar Corona saboda cutar tana da magani.

Wadannan maganganu dai da Stella tayi da kuma miliyoyin mutane suka kalla a fadin duniya sun janyo dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook cire bidiyon tare da dakatar da shafin ta a dandalin bisa dalilan da Facebook din ya bayyana da cewar yada karerayi ne game da cutar Corona.

Dandalin YouTube ma irin wannan matakin ne ya dauka inda ya toshe shafin da Stella ke anfani dashi a shafin.

Gaskiyar Magana:

A watan Yunin shekara ta 2020, hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka  da a turance ake kira US Food and Drug Administration (FDA) ta dakatar anfani da hydroxychloroquine ga masu dauke da cutar Corona a kasar.

FDA ta bayyana cewa hujjojin da ake dasu sun zayyana a fili cewa hydroxychloroquin babu gudummawar lafiya da zai iya bayarwa game da Corona, hasalima yana iya haifar da matsalolin da suka shafi zuciya.

Itama a nata bangaren, hukumar lafiya ta duniya wato World Health Organization a farkon watan day a gabata ta sanar da cewa zata dakatar da yin anfani da hydroxychloroquine da lopinavir/ritonavir akan masu dauke da cutar Corona.

Hukumar lafiyar ta bayyana cewa matakin da ta dauka din ya biyo bayan shawarwarin kwamitin kasa-da-kasa da aka kafa dan samo maganin cutar Corona ne da a turance ake kira Solidarity Trials International Steering Committee.

WHO ta bayyana cewa sakamakon binciken kwamitin ya gano hydroxychloroquine da lopinavir/ritonavir basa rage mace-macen dake faruwa sakamakon kamuwa da cutar Corona.

A martaninsa game da maganganun Stellan, Andrew McLachlan, wanda shine shugaban tsangayar nazarin magunguna na Jami’ar Sydney da a turance ake kira “Sydney Pharmacy School, University of Sydney”, ya bayyana cewa azarbabi da san birgewa ba sune abubuwan da ya kamata ayi anfani dasu ba wajen gansar da mutane cewa hydroxychloroquine yana maganin cutar Corona.

Andrew ya kara da cewa samar da maganin cututtuka yana daukan nazari da bincike mai cike da ka’idoji a matakai daban-daban.

Har wayau, Najeriya kasancewar ta daya daga cikin kasahen dake cikin kwamitin binciken wanda aka fara a watan Maris din da ya gabata ta bayyana ta hanyar Ma’aikatar Lafiya tace har yanzu bincike bai gano cewa hydroxychloroquine zai magance cutar Corona ba.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar farar hula mai suna LiveWell Initiative, Bisi Bright, LWI ne daukar nauyin wani bincike da akeyi game da gani maganin cutar Corona, sanarwar da aka wallafa shafin lafiya na jaridar Punch mai suna HealthWise, ana nazari akan mutane 123, 110 dqaga cikin wannan adadi ana kokarin karesu daga kamuwa da cutar Corona yayin da sauran 13 ake lura ko sinadarin ka iya warkar dasu daga cutar ta Corona.

Bright tace kodayake chloroquine da hydroxychloroquinesuna da rawar takawa ta bangaren lura da cutar Corona, yayi wuri a iya cewa zasu iya magance cutar ta Corona, acewarta zurzurfan bincike ne kawai zai iya tabbatar da hakan.

Itama a nata martanin, hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ta Najeriya ta hannun Dr Stella Immanuel tace ta gargadi mutane da suyi hattara wajen wajen yarda da maganin Corona. Hukumar ta kara da cewa kawo yanzu cutar bata da magani duk kuwa da cewa wassu gwaje-gwaje sun alamta cewa wassu sinadarai na iya magance cutar, amma dai riga malam masallaci ne a bayyana samun maganin cutar tunda har yanzu bincike bai fito ya bayyana hakan ba.

Stella ta karyata zancen da akeyi cewa saka takunkumin fuska baya hana kamuwa da cutar Corona.

NCDC tace saka takunkumin fuska yana taimakawa wajen kare mutane daga kamuwa da cutar Corona saboda abubuwan dake fita hanci ko baki lokacin tari.

Kammalawa:

Kawo yanzu babu kwararan hujjojin dake nuna cewa hydroxychloroquine yana maganin cutar Corona. Zargin da Dr. Stella Immanuel tayi cewa hydroxychloroquine yana maganin cutar Corona zargi ne maras tushe saboda rashin sahihancinsa a bangaren lafiya.

Hakanan maganar da Dr. Stellan tayi cewa takunkumin fuska baya kare mutane daga kamuwada cutar Corona karya ne dan binciken lafiya bai tabbatar da hakan ba.

Jawaban da Dr. Stella tayi game da cutar Corona sunci karo da nazarce-nazarce da dama a fannin lafiya da shawarwarin jami’an lafiya.

#AgujiYadaLabaranBogi

Fake News Alert! 5 Ways to Verify Information| CDD Channel