Shin Hukumar Hisbah a Jahar Ta Kama Mutane 8 Saboda Rashin Yin Azumi a Watan Ramadan?

Gaskiyar Al’amari: Eh, hakane!

Tushen Magana:

A ranar Talata, 20 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gan wani labari da ya mamaye shafukan da yawa da jaridun da ake wallafawa a yanar gizo da shafukan sada zumunta na zamani, labarin ya ce Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta kama mutane 8 maza da mata bisa cin laifin rashin yin azumi a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke yin azumtan watan Ramadan na bana. Jaridu da shafukan da suka wallafa labarin sun hada da: VanguardSahara ReportersDaily PostNairalandNaijaloadedStelladimokokorkus

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa da gaske ne Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta kama mutane 8 bisa laifin cin abinci da rana acikin watan Ramadan ba tare da wani dalili ba.

Kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Harun Ibsina ya tabbatar wa CDD kama mutanen su 8 maza da mata wadan da ya ce basu da wani karbabben dalili na rashin lafiya ko wani wani uzurin da Shari’a za ta amince dashi da zai basu damar cin abinci da rana.

Ibnsina ya kara da cewa: “mutanen da muka kama da basu da wani karbabben uzurin kin yin azumi. Da ace mahaukata ne ko marasa lafiya ko masu wani dalili da Shari’ar Musulunci ta amince dashi ba za mu kama su ba”.

“abinda mutane da yawa basu fahimta ba shine wadan da muka kama din Musulmai ne, ba za mu kama Kiristoci ba saboda cin abinci lokacin azumin watan Ramadan, ba za ma mu kama Musulman da basu balaga ba saboda rashin yin azumi ko Musulman da ke da uzurin da Shari’a ta amince dashi”

Kammalawa:

Rahoton da ake yadawa cewa hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama wasu mutane 8 saboda rashin yin azumi a watan Ramadan gaskiya ne. Kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Harun Ibnsina ya tabbatar da kama mutanen inda yace wadan da aka kama din Musulmai ne kuma marasa dalilin rashin lafiya ko wani uzuri ko dalilin da Shari’ar Musulunci tayi lamuni akansa.

CDD na jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa