Shin Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Wuraren Killace Masu Dauke Da Cutar Corona?

Gaskiyar Magana: Eh, Haka Ne!

Tushen Magana:

A ranar Juma, 11 ga Disanban shekara ta 2020, masu tanatnce sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wata kafa mai suna ireporteronline ta wallafa sun gwamnatin tarayya ta bada umarnin shirye-shiryen sake bude wuraren killace masu dauke da cutar Corona da ake dasu a fadin Najeriya sakamakon sake samun karuwar bullar cutar Corona a karo na biyu. Jigon labarin ya yace: “gwamnatin tarayya ta bada umarnin sake bude waruren killace masu dauke da cutar Corona”

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin bada umarnin sake bude wuraren da ake ajiye masu dauke da cutar Corona din gaskiya ne.

Wata sanarwa da kwamitin shugaban kasa kan cutar Corona ta fitar lokacin ganawa da manema labarai a ranar 10 ga watan Disanba, 2020 tace gwamnatin tarayya ta rufe wuraren da ake ajiye masu dauke da cutar Corona ne sakamakon karancin bullar cutar a baya amma yanzu ana kara ganin karin bullar cutar saboda haka ya zama dole a fara shirye-shiryen sake bude wuraren da masu dauke da cutar ke samun kulawa.

Da yake magana a rtaron manema labaran, ministan lafiya Osagie Ehanire ya gargadin ma’aikatan lafiya da su zauna acikin shiri sakaakon sake samun bullar cutar.

Ehinare yace: “muna kara ganin yawaitar alkaluma game da cutar a yan kwanakin nan, wannan yana nuna cewa muna daf da shiga mataki ga gaba na sake barkewar annobar cutar ta Corona. A stain day a gabata mun samu bullar cutar har sau 1843 wanda yayi sama da abinda muka samu satin da ya gabata na 1,235, haka kuma wannan adadi sama yake da abinda muka samu satin da ya wuce kafin wannan inda muka samu 1,126”

Ministan yayi gargadin cewa wannan cuta tana kisa kuma kara kaimi wajen kare mutane daga kamuwa da ita.

Ya kara da cewa:  “kasashen Amurka da Birtaniya duk sun shiga mawuyacin hali sakamakon bullar wannan cuta kuma muna jajan ta musu”.

Ministan ya kara da tunda har yanzu ba’a samu maganin cutar ba, babban abin yi shine a dauke matakan kare kai daga kamuwa da ita irin su rufe fuska da baki da hanci, wanke hannaye da sabulu mai kasha kwayoyin cutittuka ko sinadari.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya tana shirye-shiryen sake bude wuraren killace masu dauke da cutar Corona gaskiya ne. Wannan na zuwa a daidai lokacin da cutar ke sake bulla a Najeriya.

CDD na karfafawa jama’a gwiwa game da tantance game da tantance sahihancin labarai kafin yadasu.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa