Shin Gwamnatin Tarayya Na Raba Tallafin N10,500 Duk Sati Ga Yan Najeriya?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 20 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da bayanan da ake dan tantance sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sunyi kichibis da wani sako da aka kirkira kuma ake yada shit a manhajar WhatsApp. Sakon nan cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin naira dubu goma da dari biyar (N10,500) a matsayin tallafi ga yan Najeriya a kowane mako .

Sakon wanda aka yima sa lakabin: “tallafin rage radadin cutar Korona a zango cutar na biyu”,  ya bukaci jama’a da su nemi tallafin wanda a cewar sakon cika fom neman baya daukar lokaci mai tsawo.

Wannan adireshi na yanar gizo da ke neman wanda ke da sha’awar tallafin su nema yace hadakar kungiyoyiin sakai masu zaman kansu da ke bada tallafi wajen yakar cutar Korona (CA-COVID) ne ka bada tallafin. A shafin an wallafi sakonnin bogi na wassu mutane da aka bayyana su a matsayin wadan da sukaci gajiyar tallafin suna tofa albarkacin bakin su.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa babu wani tsarin tallafi da gwamnatin tarayya ke bayarwa na N10,500 ga yan Najeriya duk sati. Binciken har wayau ya bankado cewa yan danfara ne suka kirkiri adireshin yanar gizo tare da kirkiran sakon dan yaudaran jama’a.

Hotunan da za’a gani a shafin yayin da mutum ya ziyarci ce shi sun hada wadannan da za’a iya gani a sama, kuma binciken da CDD ta gudanar wadda ya shafi nazarin hotunan ta hanyar fasaha ya gano cewa an dauke su ne yayin raba kudaden tallafin Korona a yankin Kwale dake gundumar babban birnin tarayya Abuja a watan Afirilun shekara ta 2020.

Karin binciken da CDD din ta gudanar wadda ya hada ziyartan shafukan sada zumunta na hadakar kungiyoyi da masa’antu masu zaman kansu da ke taimakawa yunkurin gwamnati na yakar cutar Korona ya cewa hadakar bata da wani shiri na bada tallafin N10,500 ga yan Najeriya.

Kammalawa:

Wani sako da ake yadawa cewa gwamnatin tarayya na bada tallafin N10,500 ga yan Najeriya duk sati karya ne. Sakon wani tarko ne da yan damfara suka tsara dan cutar jama’a, dan haka CDD na jan hankali mutane da su gujewa amincewa ko yada sakon.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku a kansu dan tantance muku ta wannan lamba: +2349062910568 ko ta shafin Twitter: @CDDWestAfrica/@CDDWestAfrica_H

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa