Shin Gwamnatin Kano Ta Canzawa Titin Faransa (France Road) Suna?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

A ranar 5 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) suka gano wani rubutaccen sako da aka yada ta hanyar WhatsApp dake cewa gwamnatin Kano ta canzawa titin Faransa (France Road) suna zuwa titin Madina (Madina Road).

Kamar yadda sakon wanda aka rubuta cikin harshen Hausa ya bayyana, dalilin canza sunan ya biyon bayan kalaman batanci da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayi ga addinin Musulunci.

Sakon ya yabawa gwamnatin Kano bisa kudurin sannan ya nemi jama’a suyi biyayya game da canjin da akayin.


Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa labarin ake yadawa cewa gwamnatin Kano ta canzawa titin Faransan (France Road) karya ne!

Ziyarar da CDD takai zuwa titin na Faransa ta gano cewa babu wata alama dake nuna canzawa titin suna.

Hakanan hakanan da yake bada ba’asi game da labarin, kwamishinan yada labarai na jahar Kano, Muhammad Garba yace gwamnatin Kano bata canja sunan titin ba.

Garba yace: “har yanzu babu sanarwa a hukumance dake nuna canja sunan, gwamna baya nan, hukuma bata dauki matsaya ba”.

Kammalawa:

Gwamnatin Kano bata canja sunan titin Faransa (France Road) ba sakamakon kalaman batanci da shugaban kasar Faransa yayi ga addinin Musulunci.

Titin yana nan a sunan sa da aka sanshi na Faransa. CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa