Shin an Jikkata Uwargidan Gwamnan Jahar Ondo Tare Da Kashe Wassu Mutane Uku Yayin Da Taje Kada Kuri’arta?

Gaskiyar Magana: Karya Ne!

Tushen Magana:

Wani bidiyo da aka yada a shafin Twitter a ranar Asabat, 10 ga watan Oktoban shekara ta 2020 ya bayyana cewa an raunata uwargida gwamnan jahar Ondo, Betty Anyanwu-Akeredolu  tare da hallaka wassu mutane uku da safiyar ranar yau lokacin da taje kada kuri’arta a runfar zabe mai lamba 5 a akwati mai lamba 6 dake gundumar Owo.

Bidiyon da aka yada din yana dauke da alamar gidan talabijin na Channels. Labarin da aka yada din ya kuma ce jami’an tsaro sun mamaye mazabar da Betty taje kada kuri’arta.

Tsohon Sanata Dino Melaye da shafin jam’iyyar PDP (@OfficialPDPNig) sun yada wannan bidiyo kodayake tuni wadannan kafafen suka goge wannan bidiyon daga shafukan su.

Gaskiyar Magana:

Tantancewzr da CDD ta aiwatar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro basu mamaye mazaba mai lamab 6 a gunduma ta biyar dake karamar hukumar Owo a jahar Ondo ba.

Hakanan ba’a raunata uwargidan gwamnan jahar Ondo wato Betty Anyanwu-Akeredolu ba kuma ba’a kashe wassu mutane uku ba kamar yadda wani bidiyo da aka yada a shafin Twitter a ranar Asabat, 10 ga watan Oktoban shekara ta 2020 yayi zargi.

Masu lura da yadda kada kuri’a ke gudana da CDD ta baza a jahar Ondo suna wannan mazaba kuma sun tabbatar da cewa babu wani abu mai kama da haka day a faru.

Karin tantancewa da CDD ta aiwatar ya gano cewa wannan bidiyo da aka yada an dauke shi ne a jahar Delta (a ranar 3 ga Oktoban shekara ta 2018) kuma tashar talabijin ta Channels c eta daukeshi lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Taken rubutu da aka yiwa bidiyon tun farko shine: “Zaben Fidda Gwani na Yan Majalisar Tarayya na Jam’iyyar PDP”.

Har wayau masu lura da kada kuri’a na CDD sun nadi bidiyon maid akin gwamnan yayin da take karyata faruwar raunata tad a kashe wassu mutane ukun.

Da take Karin bayani wa yan jarida, Betty Anyanwu-Akeredolu tace: “wannan shiririta ne da rashin hankali, kuma wannan yana nuna yadda wadannan mutane suka zaqu”.

Betty ta cigaba da cewa: “ina nan cikin walwalar jama’a amma wani yana can yana sauya fasalin wani bidiyo dan ruda mutane”.

Kammalawa:

Bidiyon da ake yadawa cewa an raunata uwargidan gwamna Akeredolu na jahar Ondo tare da kashe wassu mutane uku yayin da taje kada kuri’arta bidiyo ne na karya!

CDD tana jan hankalin mutane da su guji yarda ko amincewa da dukkan labaran da suka ji musamman wadan da suka fito daga kafafen sadarwa marasa tushe na dandalolin sada zumunta na zamani.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa