Labaran Karya da CDD ta Gano Tare da Binciko Sahihancin Su a Mako na Biyu, Watan Afrilu, 2021

Aikin mu a Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) shine ganowa tare da binciko gaskiyar labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani dama kafafen yada labarai. A makonni biyun da suka gabata, masu bin diddigin labarai dan gano sahihancin su na CDD sun bankado wasu labaran karya da aka wallafa tare da yada su a shafukan Facebook da Twitter da manhajar WhatsApp.

Labaran da CDD ta gano din sun hada da labarin bogi da aka yada cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama tare da cin tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna rayuwa a daki daya tarar  naira dubu ashirin kowanen su, da Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya da dai sauran su:

Hukumar Hisbah a Jahar Kano Bata Ci Tarar Daliban Jami’ar Bayero N20,000 Ba!

A ranar 6 ga watan Afirilun shekara ta 2021, wani ya bulla daga kafafen yada labarai na yanar gizo da yawa. Labarin ya ce Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su sakamakon kama su da laifin zama a daki daya duk da kasancewar sub a ma’aurata ba.  Majiyoyi sun hada da: Sahara ReportersTori.ngKanyiDailyNigerDeltaConnectNaijaNewsAllSchoolsForum.

Labarin ya ce: “Hukumar Hisbah a Jahar Kano ta Bukaci Daliban Jami’ar Bayero Maza da Mata Su Biya N20,000 Dan Yin Belin Kansu Bayan Aikata Laifin Zama a Daki Guda”

Labarin da ake yadawa cewa Hukumar Hisbah a jahar Kano ta ci tarar daliban Jami’ar Bayero maza da mata da ta samu suna zama a daki daya naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su karya ne. Hisbah bata ci tarar kowane dalibi ba. Labarin da ke yayata cin tarar daliban labari ne na bogi. Domin karanta cikakkiyar laari latsa nan

Tantancewar Da CDD Ta Aiwatar: Ba a Yiwa DIG Moses Jitoboh Ritaya Ba

Masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ranar 7 ga watan afrilu sun kuma gano wani labari da ya janyo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafin Twitter. Labarin ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kebe a mataimakin Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya DIG Moses Jitoboh dan shekaru 52 a gefe guda inda ya nada Usman Alkali Baba dan shekaru 57 a matsayin sabon Sipeta Janar na Yan Sandan Najeriya.

Labarin ya kara da cewa DIG Jitoboh yana gaba da Usman Alkali a matsayi kuma an nada Alkalin ne dan tabbatar da cewa Musulmi kuma dan arewacin Najeriya ne ya hau mukamin Sipeta Janar din.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa DIG Moses Jitoboh baya gaban DIG Usman Alkali a mukami.

Binciken CDD din ya kara gano cewa Usman Alkali Baba wadda yanzu shine sabon Sipeta Janar din Yan Sandan Najeriya ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar ra 1988 yayin DIG Jitoboh ya fara aikin dan sanda a 1994. A kwanan baya ne DIG Jitoboh ya samu mukamin mataimakin Sipeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya.

Da yake maida martani kan batun, mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya ce labarin da ake yadawa cewa an yiwa DIG Jitoboh ritaya da aiki labari ne na karya. Domin karin bayani latsa nan

Minista Sadarwa Bai Ce Rashin Yin Rijistar NIN Zai Janyo Daurin Shekaru 14 a Gidan Yari Ga Mutane Ba

Masu bin diddigin labarai da gano sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da tarin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani suka wallafa. Labarin ya ce Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargadi jama’a game da fuskantan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari idan suka gaza yin rijistar NIN.

Kamar yadda labarin ya zayyana, Pantami ya furta hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da sashin yada labarai na fadar shugaban kasa ya shirya ranar Alhamis din da ta gabata.

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin.

Nazari da binciken da CDD ta gudanar game da labarin da ake yadawa cewa Ministan Sadarwa yace duk wadda baiyi rijistar NIN ba zai fuskanci zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 ya gano an jirkita labarin. Domin karin bayani latsa nan

Shugaban Kamfanin Kera Ababen Hawa na Innoson Wato Innocent Chukwuma Bai Mutu Ba!

A ranar 4 ga watan Afirilun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wani shafin yanar gizo ya wallafa inda ya ce, shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wadda kuma shine shugaban kungiyoyin fararen hula na Najeriya, Innocent Chukwuma ya mutu.

Shafin yanar gizon ya bayyana cewar abokan Chukwuma ne suka ayyana rasuwar tasa bayan yayi fama da rashin lafuyar da ke alaka da sankarar jini.

Binciken CDD ya gano cewa shugaban kamfanin kera ababen hawa na Innoson wato Innocent Ifediaso Chukwuma bai mutu ba kamar yadda shafin yanar gizon ya rawaito.

Har wayau, CDD ta gano cewa Chief Innocent Ifediaso Chukwuma bai taba kasancewa shugaban kungiyoyin fafaren hula na Najeriya ba, hasalima shi dan kasuwa ne.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an tafka kuskure wajen bayyana rasuwar daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafaren hula na Najeriya kuma Daraktan Ford Foundation West Africa, Innocent Chukwuma wadda ya mutu ranar 3 ga watan Afirilun shekara ta 2021. Domin Karin bayani latsa nan

CDD na shawartar kafafen yada labarai kan zurfafa bincike da tattara gaskiya labarai kafin wallafa su. Haka nan ana jan hankalin jama’a kan tantance sahihancin labari kafin yada shi ga sauran mutane.

Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akan su dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako SMS ko ta manhajar WhatsApp akan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter ta wannan adireshi: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafa su

  1. bill gates bai ce maganin cutar korona zai canza kwayoyin halittar danadam ba
  2. joe biden bai umarci hukumar shigi da ficin amurka ta bada izinin aiki da zama ta yanar gizo ga yan najeirya ba
  3. gwamnatin tarayya ba ta saye manhajar whatsapp ba
  4. sheikh sharif ibrahim saleh bai soki dakatar da abduljabbar nasiru kabara daga waazi a kano ba

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa