Labaran Karya da CDD ta Gano a Makon Karshe na Watan Fabrairun Shekara ta 2021

Hakika illolin labaran karya ko labaran bogo a fili suke. Labaran karya na iya haifar da rudani da tashin hankali dama jefa mutane cikin zulumi. Da alama masu kirkira da yada labaran bogi na cin kare su ba babbaka musamman a kafafen sada zumunta na zamani, ta yadda suke yada wadan nan labarai ta fuskoki daban-daban. Yada ire-iren wadan nan labarai na bogi musamman a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter, YouTube, Instagram dama WhatsApp a bune mai sauki amma mai cike da illoli ko matsaloli. Kokarin kare faruwar matsalolin da labaran karya za su iya haifarwa yasa Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) ke bin diddigin labarai dan gano gaskiyar su da nufin fahimtar da al’umma. Wannan mujalla za ta gabatar muku da wasu labaran da CDD ta bankado.

A wannan satin, cibiyar demokradiyya da cigaba ta bankado tare da binciko gaskiyar wasu labaran karya da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook da manhajar WhatsApp. Ga labaran nan kamar yadda wannan mujalla ta mu ta wallafa su:

Ba a Kori Fulani a Jahar Kano Ba!

A ranar Laraba, 24 ga watan Fabrairun shekara ta 2021,masu bincike na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani bidiyo da ake yadawa a manhajar WhatsApp. Bidiyon na ikirarin cewa jama’ar jahar Kano sun umarci al’ummar Fulani da subar jahar ta Kano dama arewacin Najeriya baki daya.

Dubiya da CDD ta yi, an gano cewa wannan labari ne na bogi. Hasali ma bidiyon an dauke shi ne lokacin wata hatsaniya da ta faru a garin Billiri da ke jahar Gombe. Hatsaniyar ta barke ne tsakanin wasu kabilu sakamakon takaddama game da nadin basaraken gargajiya da ake yiwa lakabi da “Mai Tangale” bayan rasuwar wadda ke kan mukamin. Latsa nan dan karanta cikekken labarin.

Shin WHO Ta Sauya Matsayin Ta Game Da Killace Kai da Bada Tazara?

Gaskiyar Al’amari: Karya Ne!

A ranar alhamis, 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba, sun gano labari da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sauya matsayin ta game da ka’idojin kare kai daga kamuwa da cutar Korona.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa labarin da ake yadawa game da WHO cewa mutanen da suka kamu da cutar Korona basa bukatar killace kansu karya ne.

Hukumar WHO bata ce mutanen da ke dauke da cutar Korona basa bukatar killace kansu ba. Wannan labarin hasalima an taba yadashi a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2020 inda mutane da dama sukayi ta cece-kuce akansa. Domin karanta cikekken labarin latsa nan

Babu Wani Tsarin Bada Tallafi Daga Gidauniyar Dangote

Wani sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke cewa Gidauniyar Aliko Dangote na bada tallafin kudi ga yan Najeriya masu sa’a dan fara sana’o’i a shekara ta 2021 sako ne na bogi. Yan damfara kan tsara ire-iren wadan nan sakonni da nufin tattara bayanan mutane dan zambatan su a karshe.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi. Domin karanta cikekken binciken da CDD ya gano, latsa nan.

Gwamnatin Jahar Kano Ba Ta Rushe Makarantar Sheikh Abduljabbar Ba!

Labarin da kafafen da yada labarai da yawa suka wallafa cewa gwamnatin jahar Kano ta rushe makarantar Sheikh Abduljabbar karya ne. Ziyarar da CDD takai wurin da akayi rusau din da karin binciken da ta gudanar ya gano babu abinda ya samu makaranta ko masallacin malamin.

CDD na tabbatar da cewa wannan labari ne na bogi dan haka jama’a suyi watsi dashi.

CDD na jan hankalin kafafen yada labarai da jama’a da su guji yada labaran karya ko wadan da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku gaskiyar su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568. Samu karin  bayani anan.

Wasu daga ciki labaran karya da CDD ta bankado tare da wallafawa

  1. babu wani tsarin bada tallafi daga gidauniyar dangote
  2. shafin twitter na bogi da ke alakanta kansa da maaikatar matasa da wasanni ta tarayya
  3. shin gwamnatin tarayya ta amince da yin rijistar nin ta hanyar yanar gizo
  4. gwamnatin jahar kano ba ta rushe makarantar sheikh abduljabbar ba

Domin sauke mujallar mu, latsa nan