Kananan Yara Sun Kada Kuri’a a Zaben Kananan Hukumomi Da Ya Gudana a Jahar Kano

Tushen Magana:

A ranar Asabat, 16 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigada (CDD) sun gano tarin hotuna da bidiyoyi da ke nuna kananan yara suna kada kuri’a a lokacin da ake gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar a fadin jahar Kano.

Hotunan da ma bidiyoyin an yada su sosai a shafukan Twitter da Facebook, kuma acikin su anga yara wadan da bisa doka shekarun su basu kai na kada kuri’a suna dangwala hannayen su a kuri’u yayin da jami’an zabe kalmashewa tare da jefa ta acikin akwatin zabe.

Bidiyoyin sun janyo cece-kuce da tofin alatsine daga yan Najeriya a kafafen sada zumunta na zamani.

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar dangane da hotuna da bidiyoyin ya gano cewa an bar yara sun kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da kansilolin na jahar Kano na shekara ta 2021.

Karin binciken da ya shafi fasaha da CDD din ta gudanar ya gano cewa bidiyoyi da hotunan an dauke su ne a zaben shekara ta 2021 din ya suka nuna yara kanana suna kada kuri’a a wurare daban-daban.

Daya daga cikin hotunan da yara suka kada kuri’un an dauke shi ne a karamar hukumar Kabo yayin da wani bidiyon da shima yake nuna nuna yara na kada kuri’a tare da tallafin wassu jami’an zabe aka nade shi a Shahuci da ke karamar hukumar birni dake cikin birnin Kano (Kano Municipal Council).

Bayan nazari da bincike, CDD na tabbatar da cewa kada kuri’un da yara suka yi dama yin zabe sau da yawa da wassu manya aka gani suna yi ya faru ne a gaban jami’an zabe na hukumar zabe ta jahar Kano, hasali ma anga jami’an hukumar zabe ta jahar Kano (KANSIEC) din suna taimakawa yaran da manya masu zabe fiye da sau daya.

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa akwai hotunan zaben shekara ta 2018 da aka gudanar na kananan hukumomi a jahar Kano din da wassu mutane suka sake yada su tare da bayyana su a matsayin hotunan zaben shekara ta 2021.

Wannan hoto da ke kasa da wani shafin Twitter mai suna @Ayemojubar hoto ne da aka dauke shi lokacin zaben kananan hukumomi na shekara ta 2018 a jahar Kano.

Kammalawa:

Wadan su daga cikin hotuna da bidiyoyin da suka nuna yara kanana suna kada kuri’a lokacin zaben kananan hukumomi na shekara ta 2021 a jahar Kano hotuna na ne gaske, al’amarin ya faru. Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa an bar yara kanana sun kada kuri’a tare da barin sauran wassu mutanen su kada kuri’a sau da daya.

Binciken CDD ya gano cewa masu anfani da kafafen sada zumunta na zamani sun yada hotunan kananan yara na kada kuri’a wadan da aka dauka a zaben day a gabata na shekara ta 2018 lokacin wannan zabe na shekara ta 2021.

CDD na jan hankalin jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su ga sauran mutane a kowane lokaci.

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa