Hoton Da aka Ga Shanu Na Cin Timatir a Gefen Hanya Ba a Najeriya aka Dauke Shi Ba!

Tushen Magana:

A ranar 2 ga watan Maris din shekara ta 2021, wata mai amfani da dandalin Facebook mai suna Amanda Chisom ta wallafa wani hoto day a nuna wasu shanu na cin wani tumatir mai tarin yawan gaske da ke jibge a gefen hanya.

Hoton ya alamta cewa an dauke shi ne a arewacin Najeriya kuma shanun na cin tumatir din ne sakamakon dakatar da kai kayan abinci kudancin kasar nan. Da yawan masu amfani kafafen sada zumunta na zamani sun kara yada hoton inda suka nuna cewa al’amarin ya faru ne a arewacin Najeriya, kuma abinda ya janyo hakan shine matakin dakatar da kai kayan abincin kudancin Najeriya da yan kasuwa na arewa da direbobi suka dauka.

Wanda da ya yada hoton a shafin Twitter shine Spartan – El Pluribus Unum! (@Osegun_MG), har wayau Reno Omokri, tsohon mai taimakawa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya wallafa hoton a shafin Nairaland.

Gaskiyar Magana:

Tarin tumatirdin da aka gani shanu suna cin a gefen hanya ba a Najeriya aka dauke shi ba. Funny, wani shafin yanar gizo da ke kasar India ne ya fara wallafa hoton ranar 30 ga watan Yulin shekara ta 2017.

A ranar 9 ga watan Janairun shekara ta 2021, wani shafin Twitter mai lakabin @Rukhsar428 ya wallafa hoton da wasu hutunan inda suka bayyana cewa matakan da gwamnatin nan ke dauke a bangaren tattalin arzikin kasa basu da alfanu ga bangaren.

A watan Janairun shekaran nan, masu amfani da shafin Twitter sun wallafa hoton yayin gangamin neman dakatar da shigo da tumatir kasar India, anyiwa gangamin lakabin: #StopImportTomatoAndOnion

Kammalawa:

Wani hoto da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani inda aka ga shanu na cin tarin tumatir da aka zubar a gefen hanya ba a Najeriya aka dauke shi ba. Wani shafin yanar gizo mai lakabin Funny ne ya fara wallafa hoton a kasar Indiya a ranar 30 ga watan Yulin shekara ta 2017.

CDD na jan hankalin jama’a da su guji yada duk abubuwan da ba su tantatnce sahihancin su ba.

Za ku iya turowa CDD labaran da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta hanyar aiko gajeren sako ko ta manhajar WhatsApp akan lamba: +2349062910568 ko a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa