Gwamnatin Tarayya Bata Bada Umarnin Bude Dukkan Makarantun Sakandare a fadin Kasa Baki Daya Ba

Tushen Magana:

A ranar 27 ga watan Yulin shekara ta 2020, zauruka da shafukan yanar gizo da yawa sun wallafa wani labari da ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bada umarnin cigaba da karatu da bude  makarantun sakandare a fadin kasarnan baki daya ranar 4 ga watan Agustan nan.

Labarin wanda aka rubuta shi kamar haka: “Labari da dumu-dumin sa: gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude makarantun sakandare a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 2020”, yayi ikirarin cewa daraktan yada labarai da hulda jama’a na ma’aikatar ilimi ta kasa ne ya sanya hannu a takardar umarnin bude makarantun.

Gaskiyar Magana:

Gwamnatin tarayya bata bata umarnin bude makarantu sakandare ba. Umarnin kawai da gwamnatin tarayyar ta bayar shine na bude ajujuwan da dalibai ke rubuta jarabawa, kuma wadannan ajuju sune: aji shida na babbar sakandare wato SS3 da kuma aji uku na karamar sakandare wato JSS3

Kodayake jigon labarin yace makantun sakandare da nufin duk dalibai, wani bangare na gundarin labarin ya bayyyana cewa daliban dake rubuta jarabawar kammalawa ne kawai zasu dawo dan fara rubuta jarabawar WAEC da za’a fara ranar 17 ga watan Augustan shekara ta 2020.

Har wayau wani jawabi da aka wallafa a shafin Twitter na ma’aikatar ilimin ta tarayya yace: “sanarwa: dalibai masu kammala sakandare zasu dawo makaranta a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 2020.

Kammalawa:

Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba na shawartan jama’a da su rika karanta labari sosai saboda a lokuta da dama jigon labari yana haifar da rudani dangane da sakon da labarin ke isarwa.

Dalibai masu kammala karantu a matakin sakandare ne wato wanda zasu rubuta jarabawar WAEC zasu dawo makaranta dan fara jarabawar su a ranar 17 ga watan Agustan shekara ta 2020.

Kada a rika sauran yada labari musamman idan ya fito daga zaurukan da suka saba yada gulmace-gulmace dama wassu kafafen sada zumunta na zamani. Hakanan a rika tantance sahihancin labari kafin yadashi.