Bidiyon Dake Nuna Jagororin Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Kasa ASUU Suna Dambe Bidiyo Ne Na Bogi!

Tushen Magana:

An wallafa wani bidiyo a shafin Twitter a ranar Asabat, 24 ga watan Oktoban shekara ta 2020 kuma acikin wannan bidiyon anyi ikirarin cewa shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU yasha mari daga yan majalisar tarayya. Mutane da yawa sunyi tsokaci akan bidiyon hakanan wassu zaurukan yanar gizo sun wallafa shi. Zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoto, mutane sama da dari ne suka ce bidiyon ya burgesu yayin da wassu mutanen 74 suka bada nasu ba’asin.

Gaskiyar Magana:

CDD ta gano cewa bidiyon da aka yadawa din akace jami’an kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ne suke fada bidiyo ne na karya. Gaskiyar al’amari itace bidiyon ya nuna hatsaniya ce da ta faru a majalisar dokokin jahar Edo a shekara ta 2017. Daya daga cikin wadanda suka wallafa wannan bidiyo wanda kuma shafin na witter ya tantance sahihancin sa shine @GoldmyneTV.

Karin binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Sahara Reporters ne suka fara wallafa bidiyon a shafin su na YouTube a ranar 14 ga watan Agustan shekara ta 2017 kuma an yada wannan bidiyon sosai.

An dauki bidiyon ne lokacin da aka samu hargitsi da takai ga bawa hamata iska tsakanin yan majalisar lokacin da aka tunbuke shugaban majalisar Justine Okonoboh bayan da takwarorin sa yan majalisa 16 suka amince da cire shin. Cire shin ya biyo bayan zargin keta ka’idojin aiki day an majalisar ke tuhumar sa da aikatawa.

Wani abinda CDD ta gano shine, bidiyon na ainihi yana da tsawon minti 2 ne amma sai aka yanki wani bangaren sa mai tsawon dakika 27 akayi anfani dashi dan nuna cewa jagororin ASUU ne ke takaddama.

Daya daga cikin mutanen da aka gani acikin bidiyon yana jefawa dan uwansa dan majalisa wani abu shine tsohon wakili a majalisar jahar Edon Hon. Kabiru Adjoto.

Wani abinda CDD ta gano shine a karshen bidiyon anga daya daga cikin mutanen dake danbe da junan su yana kokarin daukan sandan majalisar.

Kari akan bayanan da suka gabata a sama shine yadda babu wata kafar yada labarai da ta rawaito ko bada labarin cewa jagogorin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU sunyi danbe da junan su.

Kammalawa:

Rade-radin da akeyi cewa mutumin da aka gani ana shararawa mari acikin wani bidiyo shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ne karya ne! Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa mutumin cikin bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani ba shugaban kungiyar ASUU bane.

Bidiyon da ake yadawan tsohon bidiyo ne kuma a dauke shi ne a shekarar 2017.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa