Shin Mai Alfarnma Sarkin Musulmi Ya Bayyana Jagororin Arewa a Matasyin Marasa Tunani?

Tantancewar CDD: Sarkin Musulmi Bai Fadi Hakan Ba!

Tushen Magana:

A ranar 25 ga watan Agustan shekara ta 2020, masu tantance sahinhancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da jaridar Nigeria Pilot ta wallafa da kuma aka yada a dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook dake cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyyana jagoraori da mahukuntan arewa a matsayin marasa hankali. Jaridar ta gina labarin da taken: “Arewa tana da kamai in banda hankali”.

Wani bangare na labarin yace: Mai Alfarma Sakin Musulmi kuma shugaban majalisar koli da harkokin addinin Musulunci wato Alhaji Sa’ad Muhammad Abubakar ya zargi jagororin Arewa da rashin gaskiya da tunani da aiwatar da manufofi da kuma rashin karsashin tsara al’umma dan cigaban kowa.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa taron tattauna matsalolin tsaro ya gudana a ranar 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2020 a Kaduna bisa shiryawar kungiyar farar hula mai suna Arewa Research and Development Project (ARDP).

Labarin da Nigeria Pilot din ta wallafa ya zargi Sarkin Musulmin da yin kalaman a ranar 25 ga watan Augustan shekara ta 2020, amma hakan ba gaskiya bane duk kuwa da jaridar nemi ruda mutane da sasu su yarda cewa kalaman sun faru ne a baya-bayanan.

Wata gaskiyar da CDD ta kara bankadowa ta gano cewa Sarkin Musulmin yayi wassu maganganu dan jan hankalin mahukuntan arewa game da matsalolin ta lokacin taron nemo mafita ga yankin akan baarazanar taso. Sarkin Musulmin a wancan lokacin ya bayyana cewa Arewa bawai ta rasa mafita ga matsalolin ta bane, abinda yankin ya rasa acewar sa shine rashin aniya ta kwarai daga mahukunta wajen aiwatar da manufofi da shawarwarin da zasu fitar da yankin daga matsalolin sa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya shawarci shugabannin arewan musamman gwamnoni das u aiwatar da shawarwarin nazarce-nazarcen da akayi dan fitar da yankin daga tarin matsalolin sa.

Kammalawa:

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar baice jagororin arewa basu da hankali ba. Gaskiyar magana itace Sarkin Musulmin ya shawarci mahukunta musamman gwamnonin arewa da su aiwatar da shawarwarin nazarce-nazarce da aka gudanar dan fitar da yankin daga matsalolin da yake fuskanta, kuma ya bada wannan shawara ne a watan Fabrairun shekara ta 2020 ba a ranar 25 ga watan Agustan da muke ciki ba kamar yadda Nigeria Pilot ta rawaito.

CDD tana jan hankalin jama’a da suyi watsi da wannan labari tare da karanta labarai a tsanaki a kowane lokaci da tantance labaran bogi daga sahihai. Akiyaye dan zaurukan suna da al’adar yada labaran bogi dan samun karuwar masu ziyartar shafukan su.

Kuna iya aikowa CDD labarai dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2348062910568 ko ta shafin mu na Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa